Tuesday, 20 January 2026

GUMBAR DABINO



 GABATARWA da sunan ALLAH mai rahma mai jin ƙai tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina ƙara godewa ALLAH bisa dama daya sake bani domin isarda wannan saƙon fatana al ummar annabi su amfana sannan duk wanda ya karanta shima yayi ƙoƙarin isar dashi ga wasu NAGODE.

A daidai lokacin da ƙimah da mutuntaka ke kan gaba wajen jan ragamar auren kowacce mace a wannan zamanin yayinda take kokari da fafutukar karesu domin zaman lafiyar ta, sai gashi wasu matan tun kafin aurensu suke rasa wannan damar,

A lokacin da kike tareda saurayinki komai shauƙin soyayya kada ki fifita ƙawa zuci akan sanin yakamata wannan shine ake ƙira mutuntaka, domin kinada wata daraja babba a wajen wanda zai aureki itace rashin saninki a matsayin ƴa mace wannan darajar ba kowacce mace ke iya ganeta ba, amma da zaran ya kusanceki kafin aure to zaifi miki kwanciyar hankali ki rabu dashi ki auri wani,

domin kin rasa babban abu mafi muhimmanci da namiji keso ajikinki, Kin rasa kimah a wajensa bazai taɓa yarda dake akan dashi kaɗai kika taba saduwa ba, ki sani zai shafe tsawon rayuwar aurenku yana zarginki,

Kin rasa budurcinki wanda idan har bai aureki ba kin shiga wani yanayi wanda kowanne irin magani kikayi bazaki taɓa dena fargabar hakan ba har sai bayan kinyi aure kinga meya faru a daren farko, Kin rasa zumuɗin namiji akan mace wanda wannan kaɗai ke bawa amarya damar riƙe miji a hannu, bazaiyi zumuɗi akan ki ba saboda abunda ake zumuɗi akansa ya sanshi tun kafin aure

Kin ɗauki zunubi wanda girmansa yakai yasa ki rasa farinciki na har abada matuƙar baki dage da tuba ba wannan zunubin bazai bari ki samu farin ciki duniya da lahira ba, Waɗannan manyan kalubalen fa duka a dalilin kuskurenki ɗaya wanda da kin hakura dashi lokacin da ya nemiki da zina ba abunda zai sameki, idan saurayinki ya fasa aurenki saboda kinki yarda kuyi zina to dama ba aurenki zaiyi ba, Siririn layi ne ya banbanta farin ciki da baƙin ciki ko meye zai faru tsakaninki da saurayinki daga ƙarshe kece zakisha wahala,

dan haka idan kina buƙatar mutuntaka a wajen mijinki irin wanda sauran mata ke samu bayan sunyi aure to ki tabbatar babu maganar sanin ɗa namiji har sai kinyi aure,

Nayi wannan tsokacin ne domin ya zama ginshiƙi akan abunda zan rubuta na magungunan mata na gyaran jiki wanda zasu baki daraja da kimah a wajen mijinki to amma kafin nan dole kina buƙatar mutuntaka a wajensa, wannan dama ce babba ga waɗanda basuyi aureba suyi taka tsantsan, ga wanda suke matsayin matan aure kuma to damace ta gyaran jiki domin ɗorewar soyayya tareda mutuntaka.

GUMBAR DABINO


Kinada damar yin gumbar dabino ki ajiye ba tare da tayi tsami ko kuma ta lalace ba, a koda yaushe kika ɗauko zakisha abunki wannan wata dama ce ga masu koyon haɗa magani, hanyar da zakibi bayan kin gurza kwakwar kin gyara ayar saiki soyasu wato kwakwa da ayar duka ki soya saiki samu dabino wanda yake a bushe yanda zaki iya ganinsa ki haɗa waje ɗaya kiyi musu daka sosai zakiga sun haɗe sun zama gumbar mata ta dabino, Adadin kayan haɗi anan matsalar take abu na farko anaso kwakwa tafi yawa sai dabino, aya itace kaɗan acikinsu, ki lura da wannan da wajen suyan domin ƙaranin kuskure zaisa ta kasa haɗewa irin gumbar.

ana damawa da madara ko nono yanda ake zuba fura a nono haka ake zubawa asha maganin ni'ima ne sosai wannan, zaki iya cinta haka nan babu nono amma dai da nonon tafi.

SIRRIKA UKU NA ZOGALE  


No comments:

Post a Comment

MATSI DA KWALLAN MAGORO

  MATSI DA KWALLAN MAGORO Rubutu da yawa da akeyi a social media kasan abune da bazai yiwuba ɗanyen ƙwallon mangwaro ace mace tasa a gabanta...