Saturday, 24 January 2026

MATSI DA KWALLAN MAGORO

 

MATSI DA KWALLAN MAGORO



Rubutu da yawa da akeyi a social media kasan abune da bazai yiwuba ɗanyen ƙwallon mangwaro ace mace tasa a gabanta ai saidai ma ya ƙara buɗeta, sannan ɗanyen mangwaro dole ɗan cikinsa zai yi ɗaci shi kuma abu me ɗaci kashe ɗanɗanon gaban mace yake,

Zaki iya matsi da ɗan mangwaro amma wanda zai miki kyau da inganci shine wanda ya nuna zaki ɓare ki yanyanka ƙwallon cikin saiki saka ƴaƴan gabaruwa ki zuba ruwa ki tafasa sannan ki sauke idan ya huce kina tsarki ko sitz beth wato kina shiga cikin ruwan da ɗuminsa kina zama, wannan yana matse mace musamman masu jego yana temakawa wajen tsaftar gaba,


MATSI DA TAFARNUWA 




Saka ƙwallon tafarnuwa a gaba ya kwana yana saka warin gaba ana so dai asaka na ɗan lokaci kaɗan a cire yana maganin sanyi me saka zubar ruwa, sannan yana riga kafin kamuwa da ciwon, saidai idan kina so kada ya shige ciki zaki iya ɗaure shi da zare me tsafta,

tafarnuwan sili guda ɗaya zaki samu amma ki tabbatar kin ɓare sai kiyi amfani da allura ki caccaka jikinta sannan ki ɗaure da zare kamar yanda kikaga wannan photon ya nuna sai ki saka zaren yana waje bayan wani ɗan lokaci saiki janyo ta, 

Giveaway 

Zaki Iya cin kyautan hadan, dan maganin gyaran nono ta hanyar masa wasu tambayoyi.


Danna nan yanxu

Shafin littafan hausa

Friday, 23 January 2026

Sirrin Soya Jijjiban Saniya


 Sirrin Soya Jijjiban Saniya


wannan shine soyayyen jijjiɓi wanda asalinsa daga garin ciccibi yake, jijjibin saniya sirrin gyaran jiki ne sosai wanda idan har mace ta iya shi sannan taci shi a a daidai lokacinda ya dace to a gaskiya babu maganar tsufa da wuri musamman abunda ya shafi gyaran gabanta,


Kamar yanda wasu suka sani shekarun baya soyayyen jijjiɓi mukeyi yayinda muke gyara asalin naman gaban saniya na karama wanda bata taba haifuwa ba ayi dafuwar da itatuwan sannan a mayar dashi soyayye lokacinda mace zataci wannan naman to ya zama akwai garin yajin ciccibi wato yajin mai jego sai tarinƙa dan gwalawa tanacin naman dashi,

MEYE BABBAN CIN SOYAYYE DA WANDA BA SOYAYYEBA


shima wanda aka soya yana wannan aikin amma shi sai wanda ta daɗe rabonta da haifuwa ko kuma budurwa ko bazawara wanda takeda wannan matsala ta buɗewa ta ciki ko matsalar rashin cikowar gaba, anaso kici koda yanka ɗaya kullum safe da yamma a ƙallah kiyi kwana 7, idan yana soye zaki iya ajiye shi sai lokacin da kikeso kici bazai lalaceba, sannan idan kinaso koda a soye yake zaki iya masa dafuwa yanda kike dafa kowanne nama domin idan har kin soyashi to kin gama masa kowanne aiki,

Kamar yanda na fada abaya karamar saniya wanda bata haifu ba ita ake samu shine asalin jijjiɓi da baya bada matsala, ana dafashi da itatuwa kamar haka.

  • sassaƙen gabaruwa
  • sassaƙen ɓaure 
  • saiwar yaɗiya 
  • sassaƙen mangwaro 
  • Garin ɗan bashanana 

waɗannan itatuwa da ake dafawa a tace ruwan wanda da wannan ruwan dashi ake dafa naman bayan ya dafu sosai sai a sauke a soyashi ana iya saka masa magi amma dai ba'a cinsa saida yajin ciccibi,




Thursday, 22 January 2026

MATA MASU JIN ZAFI LOCIN SADUWA

 MATA MASU JIN ZAFI LOCIN SADUWA










Zak samu wannan darasin a nan


Kannywood Celebrities Photos And Videos Gallery

Kannywood Celebrities Photos And Videos Gallery 

by Class Notes - Get complete lesson notes for your subject January 22, 2026




 




Join the WhatsApp group 

Tuesday, 20 January 2026

SIRRI UKU NA ZOGALE


 SIRRIN UKU NA ZOGALE


Kowacce mace tana da damar aiki da zogele ta hanyoyi uku wanda kowanne daga ciki yanada amfani wajen sauƙarda ni'ima nan take saidai abu ɗaya da zogale yake dashi shine ɓata ciki, 

yakan sanya gudawa a kowanne lokaci shiyasa yakeda muhimmaci kisan abu buyu, kafin ki fara.

na farko shine kada kisha da yawa na biyu kuma idan kinada ƙaramin ciki wanda be wuce watanni biyar ba kadama kisha, 

amma dai wani abu kuma daya kamata kisani shine bayan ni'ima dazai baki zai ƙara miki lafya,

hanya ta farko kiyi garin zogale wanda ya bushe a inuwa saiki zuba cokali ɗaya a ruwan zafi ki bari ya jiƙa saiki tace ruwan ki saka masa madara saiki sha, 

hanya ta biyu ganyen zaki tafasa da kananfari sai bayan ya tafasa saiki tace ruwan sannan ki saka lefton kisha kamar yanda kike shan shayi,

hanya ta ƙarshe wato ta uku shine ki dafa ganyen saiya dafu saiki yanka masa farar albasa da tumatir kina iya saka masa mai da magi amma banda abu me yaji, 

kamar yanda na faɗa asama kowanne daga ciki zakiyi kada kiyi da yawa sannan sai kina tare da miji zakiyi haka kuma ba'a yinsa asaka a firji don yayi saniyi,

 saidai kina iya sakawa shayin sikari ko zuma ko mazarƙwaila don yayyi zaƙi amma dai ba'aso yayi sanyi.


MATA MASU JIN ZAFI LOKACIN SADUWA



Ko kasan cewa kana da damar shiga gasar mu domin cin kyautar waya idan ka amsa wasu tambayoyi




Domin shiga WhatsApp group na mu me suna duniyar nishadi, amma kasani wannan group din dole sai ka amsa tambayoyi sannan Zaka iya shiga.













GUMBAR DABINO



 GABATARWA da sunan ALLAH mai rahma mai jin ƙai tsira da aminci su ƙara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina ƙara godewa ALLAH bisa dama daya sake bani domin isarda wannan saƙon fatana al ummar annabi su amfana sannan duk wanda ya karanta shima yayi ƙoƙarin isar dashi ga wasu NAGODE.

A daidai lokacin da ƙimah da mutuntaka ke kan gaba wajen jan ragamar auren kowacce mace a wannan zamanin yayinda take kokari da fafutukar karesu domin zaman lafiyar ta, sai gashi wasu matan tun kafin aurensu suke rasa wannan damar,

A lokacin da kike tareda saurayinki komai shauƙin soyayya kada ki fifita ƙawa zuci akan sanin yakamata wannan shine ake ƙira mutuntaka, domin kinada wata daraja babba a wajen wanda zai aureki itace rashin saninki a matsayin ƴa mace wannan darajar ba kowacce mace ke iya ganeta ba, amma da zaran ya kusanceki kafin aure to zaifi miki kwanciyar hankali ki rabu dashi ki auri wani,

domin kin rasa babban abu mafi muhimmanci da namiji keso ajikinki, Kin rasa kimah a wajensa bazai taɓa yarda dake akan dashi kaɗai kika taba saduwa ba, ki sani zai shafe tsawon rayuwar aurenku yana zarginki,

Kin rasa budurcinki wanda idan har bai aureki ba kin shiga wani yanayi wanda kowanne irin magani kikayi bazaki taɓa dena fargabar hakan ba har sai bayan kinyi aure kinga meya faru a daren farko, Kin rasa zumuɗin namiji akan mace wanda wannan kaɗai ke bawa amarya damar riƙe miji a hannu, bazaiyi zumuɗi akan ki ba saboda abunda ake zumuɗi akansa ya sanshi tun kafin aure

Kin ɗauki zunubi wanda girmansa yakai yasa ki rasa farinciki na har abada matuƙar baki dage da tuba ba wannan zunubin bazai bari ki samu farin ciki duniya da lahira ba, Waɗannan manyan kalubalen fa duka a dalilin kuskurenki ɗaya wanda da kin hakura dashi lokacin da ya nemiki da zina ba abunda zai sameki, idan saurayinki ya fasa aurenki saboda kinki yarda kuyi zina to dama ba aurenki zaiyi ba, Siririn layi ne ya banbanta farin ciki da baƙin ciki ko meye zai faru tsakaninki da saurayinki daga ƙarshe kece zakisha wahala,

dan haka idan kina buƙatar mutuntaka a wajen mijinki irin wanda sauran mata ke samu bayan sunyi aure to ki tabbatar babu maganar sanin ɗa namiji har sai kinyi aure,

Nayi wannan tsokacin ne domin ya zama ginshiƙi akan abunda zan rubuta na magungunan mata na gyaran jiki wanda zasu baki daraja da kimah a wajen mijinki to amma kafin nan dole kina buƙatar mutuntaka a wajensa, wannan dama ce babba ga waɗanda basuyi aureba suyi taka tsantsan, ga wanda suke matsayin matan aure kuma to damace ta gyaran jiki domin ɗorewar soyayya tareda mutuntaka.

GUMBAR DABINO


Kinada damar yin gumbar dabino ki ajiye ba tare da tayi tsami ko kuma ta lalace ba, a koda yaushe kika ɗauko zakisha abunki wannan wata dama ce ga masu koyon haɗa magani, hanyar da zakibi bayan kin gurza kwakwar kin gyara ayar saiki soyasu wato kwakwa da ayar duka ki soya saiki samu dabino wanda yake a bushe yanda zaki iya ganinsa ki haɗa waje ɗaya kiyi musu daka sosai zakiga sun haɗe sun zama gumbar mata ta dabino, Adadin kayan haɗi anan matsalar take abu na farko anaso kwakwa tafi yawa sai dabino, aya itace kaɗan acikinsu, ki lura da wannan da wajen suyan domin ƙaranin kuskure zaisa ta kasa haɗewa irin gumbar.

ana damawa da madara ko nono yanda ake zuba fura a nono haka ake zubawa asha maganin ni'ima ne sosai wannan, zaki iya cinta haka nan babu nono amma dai da nonon tafi.

SIRRIKA UKU NA ZOGALE  


MATSI DA KWALLAN MAGORO

  MATSI DA KWALLAN MAGORO Rubutu da yawa da akeyi a social media kasan abune da bazai yiwuba ɗanyen ƙwallon mangwaro ace mace tasa a gabanta...