GABATARWA
da sunan ALLAH mai rahma mai jin ƙai tsira da aminci su
ƙara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina ƙara
godewa ALLAH bisa dama daya sake bani domin isarda
wannan saƙon fatana al ummar annabi su amfana sannan duk
wanda ya karanta shima yayi ƙoƙarin isar dashi ga wasu
NAGODE.
A daidai lokacin da ƙimah da mutuntaka ke kan gaba wajen jan
ragamar auren kowacce mace a wannan
zamanin yayinda take kokari da
fafutukar karesu domin zaman lafiyar ta,
sai gashi wasu matan tun kafin aurensu
suke rasa wannan damar,
A lokacin da kike tareda saurayinki
komai shauƙin soyayya kada ki fifita
ƙawa zuci akan sanin yakamata wannan
shine ake ƙira mutuntaka, domin
kinada wata daraja babba a wajen wanda
zai aureki itace rashin saninki a matsayin
ƴa mace wannan darajar ba kowacce
mace ke iya ganeta ba, amma da zaran ya
kusanceki kafin aure to zaifi miki
kwanciyar hankali ki rabu dashi ki auri
wani,
domin kin rasa babban abu mafi
muhimmanci da namiji keso ajikinki,
Kin rasa kimah a wajensa bazai taɓa
yarda dake akan dashi kaɗai kika taba
saduwa ba, ki sani zai shafe tsawon
rayuwar aurenku yana zarginki,
Kin rasa budurcinki wanda idan har bai
aureki ba kin shiga wani yanayi wanda
kowanne irin magani kikayi bazaki taɓa
dena fargabar hakan ba har sai bayan
kinyi aure kinga meya faru a daren farko,
Kin rasa zumuɗin namiji akan mace
wanda wannan kaɗai ke bawa amarya
damar riƙe miji a hannu, bazaiyi zumuɗi
akan ki ba saboda abunda ake zumuɗi
akansa ya sanshi tun kafin aure
Kin ɗauki zunubi wanda girmansa yakai
yasa ki rasa farinciki na har abada
matuƙar baki dage da tuba ba wannan
zunubin bazai bari ki samu farin ciki
duniya da lahira ba,
Waɗannan manyan kalubalen fa duka a
dalilin kuskurenki ɗaya wanda da kin
hakura dashi lokacin da ya nemiki da
zina ba abunda zai sameki, idan
saurayinki ya fasa aurenki saboda kinki
yarda kuyi zina to dama ba aurenki zaiyi
ba,
Siririn layi ne ya banbanta farin ciki da
baƙin ciki ko meye zai faru tsakaninki da
saurayinki daga ƙarshe kece zakisha
wahala,
dan haka idan kina buƙatar mutuntaka a wajen mijinki irin wanda sauran mata
ke samu bayan sunyi aure to ki tabbatar
babu maganar sanin ɗa namiji har sai
kinyi aure,
Nayi wannan tsokacin ne domin ya zama
ginshiƙi akan abunda zan rubuta na
magungunan mata na gyaran jiki wanda
zasu baki daraja da kimah a wajen
mijinki to amma kafin nan dole kina
buƙatar mutuntaka a wajensa, wannan
dama ce babba ga waɗanda basuyi
aureba suyi taka tsantsan, ga wanda suke
matsayin matan aure kuma to damace ta
gyaran jiki domin ɗorewar soyayya
tareda mutuntaka.
GUMBAR DABINO
Kinada damar yin gumbar dabino ki ajiye
ba tare da tayi tsami ko kuma ta lalace
ba, a koda yaushe kika ɗauko zakisha
abunki wannan wata dama ce ga masu
koyon haɗa magani,
hanyar da zakibi bayan kin gurza
kwakwar kin gyara ayar saiki soyasu
wato kwakwa da ayar duka ki soya saiki samu dabino wanda yake a bushe yanda
zaki iya ganinsa ki haɗa waje ɗaya kiyi
musu daka sosai zakiga sun haɗe sun
zama gumbar mata ta dabino,
Adadin kayan haɗi anan matsalar take
abu na farko anaso kwakwa tafi yawa sai
dabino, aya itace kaɗan acikinsu, ki lura
da wannan da wajen suyan domin
ƙaranin kuskure zaisa ta kasa haɗewa
irin gumbar.
ana damawa da madara ko nono yanda
ake zuba fura a nono haka ake zubawa
asha maganin ni'ima ne sosai wannan,
zaki iya cinta haka nan babu nono amma
dai da nonon tafi.
SIRRIKA UKU NA ZOGALE